Labarai
Farashin ɗanyen mai na ci gaba da faɗuwaa a kasuwar duniya

Farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya na ci gaba da faɗuwa bayan shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana cewa tattaunawar da ake yi tsakanin Iran da Amurka a ƙasar Qatar na tafiya yadda ya kamata.
Farashin ɗanyen mai na Brent ya sauka zuwa dala 71.35 kan kowace ganga, yayin da na West Texas Intermediate (WTI) ya ragu zuwa dala 68.28 kan kowace ganga.
Ana kallon tattaunawar da ake yi a Qatar na taka rawa wajen samun wannan ci gaban, lamarin da ya rage fargabar da ake yi kan yiwuwar samun tangarɗa ga samar da ɗanyen mai.
Trump ya ce dangantaka tsakanin Amurka da Iran na tafiya yadda ya kamata, inda ya ce ana ganin ci gaba a tattaunawar da ke gudanar a Qatar.
You must be logged in to post a comment Login