Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugabannin ƙananan hukumomin Kano 44 sun yi Tir da Doguwa

Published

on

Shugabannin ƙananan hukumomin Kano 44 sun yi Alla-wadai da shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya Alhassan Ado Doguwa.

Hakan na cikin wani saƙo da shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomin Kano Muhammad Baffa Takai kuma shugaban ƙaramar hukumar Takai ya aike wa Freedom Radio.

Ya ce, “A madadin shugabannin ƙananan hukumomin Kano 44, suna nuna damuwa da alhinin kan rashin ɗa’a da Doguwa ya nuna”.

“Wannan ba ita ce tarbiyyar da Ganduje da APC suka bamu ba, saboda haka muna kira ga uwar jam’iyya da ta gaggauta ladabtar da Doguwa”. A cewarsa.

Shugabannin ƙananan hukumomin sun kuma jaddada mubaya’arsu ga jam’iyyar APC.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!