Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Muhimman abubuwa 10 da Buhari ya faɗa a hirarsa da Tambari TV

Published

on

A larabar nan ne tashar Tambarin Hausa TV ta saki hirar da ta yi da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Kan hakan ne muka tattaro muku muhimman abubuwa 10 da shugaban yayi magana a kansu a tattaunawar.

Abu na farko, Shugaba Buhari ya ce Gwamnatinsa ta yi ƙoƙari wajen daƙile matsalar tsaro idan aka yi la’akari da yadda ya samu Gwamnati.

Na biyu, Buhari ya bayyana takaicinsa kan rikice-rikicen ƴan ta’adda a Arewa maso yamma, inda ya ce, abin mamaki jama’a daya addini daya amma suna yaƙar juna.

Abu na uku, Shugaban ya ce, Gwamnatinsa ta bai wa shugabannin tsaro duk abin da suke buƙata, don su kawo ƙarshen matsalolin da ke addabar wasu yankunan.

Buhari ya gargaɗe su da cewa kada su bari Najeriya ta rikice.

Batu na huɗu Buhari ya ce, a iya saninsa duk wanda aka kawo ƙara gabansa kan wasa da aiki to yana ɗaukar mataki.

Ya ce, ya sauke alƙalin alƙalai biyu, ɗaya saboda rashin iya aiki, ɗaya kuma saboda rashin lafiya.

Sai dai a wani sashen hirar ya ce, baya yiwa ɓangaren shari’a katsalandan.

Labarai masu alaƙa

Mr. Frank Geng ya musanta zargin kashe ummulkhair Buhari

Zan kawo karshen tsadar abinci kafin karewar wa’adina-Buhari

Na biyar shugaban ya jaddada cewa yana riƙe da amanar ƴan Najeriya sau da ƙafa.

Na shida, Buhari ya ce, shi ba shugaban da ya ce ba wanda ya iya sai shi ba ne, a’a ya bai wa kowanne masu ruwa da tsaki dama su yi aikinsu.

Na Bakwai, shugaban ya ce, da saninsa CBN ke shirin sauya fasalin wasu kuɗaɗen ƙasar nan.

Buhari ya ce, dalilan da CBN ya bashi shi ne, wasu sun ɓoye kuɗaɗen ƙasar nan a ƙetare, sakamakon wannan zasu dawo da shi.

Sannan ai wata uku ya isa kowa ya mayar da kuɗinsa banki indai na halal ne a cewar Buhari.

Na Takwas, ya bada tabbacin cewa za a yi zaɓe bisa adalci ba tare da murɗiya ba, kuma za bar dimokraɗiyya ta yi aiki, koda kuwa wace jam’iyya ce ta ci zaɓe.

Na Tara, ya yi alƙawarin kammala aikin hanyar Kaduna zuwa Abuja kafin saukarsa a mulki.

Na goma, Buhari ya ce, jama’a su koma gona, sannan su nemi aikin yi domin gwamnati bata da gurbin aiki, idan ma akwai bata da kuɗin da zata biya su.

KU KALLI CIKAKKIYAR TATTAUNAWAR A NAN

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!