Labarai
Shugabannin ƙasashen Afrika sun kammala taron ƙungiyarsu karo na 39 a birnin Ethiopia

Shugabannin ƙasashen Afrika sun kammala taron ƙungiyarsu karo na 39 a birnin Addis Ababa na ƙasar Habasha, inda suka tattauna game da matsalolin da Nahiyar ke fuskanta.
Shugaban kasar Burundi, Evariste Ndayishimiye da ya karbi jagorancin ƙungiyar, da takwaransa na Djibouti, Mahmoud Ali Youssouf ne suka gabatar da matsayar da taron ya cimma.
Ƙungiyar ta ce, ba za ta sake lamuntar ƙwace mulki da ƙarfin tuwo ba, a wani yanayi da shugaban mulkin sojin Guinea Janar Mamadi Doumbouya da takwaransa na Gabon Brice Nguema ke halartar taron.
Game da ƙasashen ƙawancen AES, wato Mali da Nijar da Burkina Faso kuwa, AU ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da shugabannin mulkin sojin da suka ƙwace mulki.
You must be logged in to post a comment Login