Ƙetare
Shugabannin duniya sun fara taron zaman lafiya a Paris
An buɗe taron samar da zaman lafiya da ya haɗa shugabanin ƙasashen duniya a birnin Paris na Faransa.
Taron dai ana kyautata zaton zai taimaka wajen samar da hanyoyin warware wasu daga cikin tarin matsallolin da suka addabi duniya.
Shugabannin za su shafe tsawon kwanaki uku suna tattaunawa dangane da batutuwa da dama da suka haɗa da muhalli da lafiya da na’urar zamani.
Ɗaya daga cikin batutuwan da zai fi ɗaukar hankulan shugabanin shi ne na tantance hanyoyin kawo ƙarshen annobar cutar Covid19.
Daga cikin shugabanin ƙasashen da ake sa ran za su bada gagarumar gudunmawar magance matsalolin har da shugaban Senegal Macky Sall da shugaba Mohammadu Buhari da mataimakiyar shugaban Amurka Kamala Haris sai mai masaukin baƙi Emmanuel Macron.
Ana kyautata zaton mutane dubu 15 za su kasance kai tsaye ta intanet domin kallon yadda taron zai kasance, yayin da mutane 350 za su kasance a zauren taron kuma daga cikinsu har da shugabanin ƙasashen Duniya 30, 12 daga Afrika.
RFI
You must be logged in to post a comment Login