Connect with us

Labaran Kano

Shugabar gidan talabijin na ARTV ta lashe zaben BON

Published

on

An zabi Shugabar gidan talabijin na ARTV dake Kano Hajiya sa’a Ibrahim a matsayin shugabar kungiyar kafafan yada labarai ta kasa .

 

Jaridar Kano Focus ta rawaito cewar Hajiya Sa’a Ibrahim ta kasance shugabar kungiyar a wani taro da aka gudanar na kungiyar karo na 72 , biyo bayan rashin cancanta da abokin hammayarta Yusuf Nadabo dan jihar Adamawa yayi.

 

Hajiya sa’a Ibrahim dai ita ce mataimakiyar shugabar kungiyar , kafin a zabe ta a matsayin shugabar kungiyar a yanzu.

 

Da take jawabi Hajiya Sa’a Ibrahim ta sha alwashin damawa da dukkanin mambobin kungiyar a kokarin tabbatar da cigaban kungiyar.

 

Ta kuma bayyana jin dadinta ga yadda zaben ya tafi ba tare da tashin hankali ba .

 

Zaman da kungiyar kafafan yada labarai za ta yi nna gaba za ta yi shine a Jihar Kano. An kafa kungiyar ne a 1973 a matsayin hadin gwiwar kafafan yada labarai masu zama kansu da na gwamnati.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!