Labarai
Siyawa yara littattafai zai sa su tashi da dabi’ar karatu – NCRRD
Cibiyar bincike da karfafa karatu ga kananan yara ta kasa Nigerian center for reading, research and development (NCRRD) ta ce rashin jajircewa da iyaye basayi wajen ganin yaran su sun tashi da dabi’ar san karance karancen littattafai shike kawo na kasu ga karatun yara a kasar nan.
Shugaban cibiyar reshen jami’ar Bayero dake nan Kano Farfesa Isma’ila Abubakar Tsiga , ya bayyana hakan a taron wayar dakan jama’a yadda za su kula da karatun ‘ya’yan su da hadin gwiwa da kungiyar ci gaban ilimin arewacin kasar nan
Farfesa Isma’il Abubakar Tsiga yace iyaye su ya kamata su karfafa koyawa yara karatu daga gida ta hanyar siya musu littattafai na karatu musamman idan suka nuna kwazo a makaranta, mai makon shirya musu biki ko siya musu kayan wasa a matsayin kyauta .
Ilimin ‘ya’ya mata zai gyara rayuwar al’umma –Yariman Kano
A nasa jawabin shugaban Jami’ar Bayero Farfesa Muhammad Yahuza Bello, ya ce idan har dalibi ya saba karatu tun yana yaro babu wani darasi da zai bashi wahalar koyo a manyan makarantun gaba da Sakandare.
Muhammad yahuza Bello, ya kuma ce idan yara ba’a koya musu karatuba ba zasu samu abinda suke bukata ba a harkokin koyo da koyarwa.
Taron ya samu halartar Iyayen yara da malamai da kungiyoyin kishin al’umma da dama suka halarci taron wayar da kan mutane kan lura da ilimin yaran su.
You must be logged in to post a comment Login