Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ilimi shine ginshikin cigaban rayuwa -Dagacin Bechi

Published

on

Dagacin garin Bechi ta,  karamar hukumar Kumbotso  Alhaji Lawan Yakubu Bechi,  ya bayyana ilimi a matsayin abinda ke da  muhimmanci  tare da taka gagarumar rawa, wajen cigaban al’umma.

Dagacin  ya yi kiran  ne a wajen saukar karatun Al’qur’ani mai girma na makarantar Hubbin Nabiyyi (SAW) dake garin Bechi karo na farko da dalibai goma sha uku su kayi.

Alhaji Lawan Yakubu Bechi, ya ce  ilimi ne kadai ke bada damar  samun cigaban da ake muradi a rayuwa.

Dagacin garin Kantama yayi Murabus

Bawa mata ilimi na da muhimmanci sakamakon yawansu- Farfesa Aliyu Musa

Da yake jawabi,  dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Kumbotso a wajen saukar  Mudassir Ibrahim Zawachiki,  ya bukaci  iyayen yara  dasu kara sanya idanu wajen ganin ya’yansu sun samu ilimi mai nagarta.

Shamsu Dau Abdullahi, wakilin mu da ya halarci taron  ya rawaito cewa daliban da suka sukayi haddar ta sauka, akwai masu  wadanda suke da izifi talatin -talatin da kuma goma goma.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!