Labarai
sojin Isra’ila sun kashe babban jami’in Hezbollah Haytham Ali

Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta kashe babban jami’in ƙungiyar Hezbollah Haytham Ali Tabatabai a wani hari da ta kai Beirut babban birnin Lebanon wanda aka bayyana a matsayin shugaban rundunar Hezbollah.
Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce aƙalla mutum biyar aka kashe a harin tare da raunata wasu 28.
Rahotonni sun bayyana cewa, wannan ne karon farko da Isra’ila ta kai hari Beirut cikin wata ɗaya.
Kawo yanzu babu wata sanarwa mai tabbatar da iƙirarin na dakarun Isra’ila, ko daga Hezbollah ko kuma daga gwamnatin Lebanon.
You must be logged in to post a comment Login