Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Sojoji sun bankaɗo haramtattun mata tun mai a Niger Delta

Published

on

Dakarun rundunar sojin Nijeriya sun gano wasu haramtattun matatun mai har guda 50 a dajin Biseni da ke yankin ƙaramar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa.

Kwamandan rundunar haɗin gwiwa ta Operation Delta Safe da ke gudanar da aiki a yankin Neja Delta, Rear Admiral John Okeke, wanda kuma ya jagoranci samamen ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Ya ce, a ranar 9 ga watan Mayu, sun kai samame ƙaramar hukumar Ukwa ta Yamma da ke jihar Abia kan iyaka da Rivers, ya kuma ce za su ci gaba da kai irin wannan samame domin gano wasu matatun mai da ake gudanar da su ba bisa ƙa’ida ba.

Ya ƙara da cewa, sun gano wani rami da aka haƙa a ɗaya daga cikin haramtattun matatar man wanda ke iya ɗaukan manyan motoci 10 maƙare da duro-duro na iskar gas inda kuma suke ajiye ɗanyan mai wanda daga nan kuma su riƙa shigar da shi wurin girke-girkensu.

Rear Admiral John Okeke ya ƙara da cewa za su ci gaba da kai irin wannan samame domin fatattakar masu fasa-ƙwaurin mai a yankin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!