Labarai
Sojoji sun ceto mutane 9 ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a hanyar Ajaokuta zuwa Itobe

Rundunar Sojin Najeriya ta ce, ta ceto mutane tara da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan hanyar Ajaokuta zuwa Itobe a jihar Kogi.
Rahotonni sun bayyana cewa, Sojojin sun yi artabu da masu garkuwar ne a kusa da garin Adumu, lamarin da ya tilasta musu tserewa tare da barin mutanen da suka sace.
Wadanda aka ceto din, sun haɗa da dattawa maza biyu sai mata biyu, maza huɗu da jariri
Rundunar sojin ta kara da cewa, ta miƙa mutanen da ta ceto din ga jami’an ‘yan sanda domin ci gaba da gudanar da bincike.
You must be logged in to post a comment Login