Labarai
NiMet ta yi gargadi kan yiwuwar samun ambaliya a jihohi 13

Hukumar Kula da hasashen Yanayi ta kasa NiMet, ta yi gargadin yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu jihohi 13 tsakanin ranakun 11 zuwa 20 ga watan nan da muke ciki na Agusta.
Jihohin da hukumar ta yi wannan gargadi a kansu, sun haɗa da Sokoto da Zamfara da Kebbi da Neja da Kaduna sai Nasarawa da Adamawa da Filato.
Sauran su ne: Benue da Kogi da Taraba, sai Cross River da kuma Akwa Ibom.
Haka kuma, hukumar ta NiMet, ta shawarci jama’a da su bi hasashen yanayi, tare da kauce wa shiga wuraren da ambaliyar ruwa ta mamaye, tare da kasancewa cikin shirin ƙaura zuwa wuraren da suka fi aminci idan bukatar hakan ta taso.
You must be logged in to post a comment Login