Labarai
Sojoji sun hallaka jagoran ƴan bindiga Junaidu Fasagora
Dakarun sojin Nijeriya da ke gudanar da aikin yaƙa da yan ta’adda a jihar Zamfara, sun kashe gawurtaccen jagoran ƴan bindigar nan Junaidu Fasagora tare da wasu yaransa.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta wallafa a kafar Internet.
Sanarwar ta ruwaito cewa dakarun sun samu wannan nasara ne bayan da suka fafata ta hanyar yin musayar wuta da bata garin a yankin ƙaramar hukumar Tsafen jihar Zamfara.
Haka kuma, sanarwar, ta bayyana cewa, “Junaidu Fasagora tare da sauran ƴan bindiga abokansa sun dade suna garkuwa da mutane tare da aikata wasu ayyukan ta’addanci ga al’ummar jihohi da dama na yankin arewa maso yammacin kasar.”
“Wannan gagarumar nasara ce a yaƙin da ake yi da ta’addanci da kuma rashin tsaro” in ji sanarwar.
You must be logged in to post a comment Login