Labarai
Sojoji sun hallaka yan bindiga 14 a Katsina

Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka wasu mutane 14 da ake zargi ’yan bindiga ne a wani samame da suka kai a garin Gora, Ƙaramar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne a daren ranar Talata, inda sojojin suka kuma ƙwato babura bakwai da ake zargin ’yan bindigar na amfani da su.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa ’yan bindigar sun shiga garin ne da yawa a kan babura, ɗauke da makamai, da niyyar kai hari a yankin.
Sai dai majiyoyin sun ce jami’an sojin da suka samu bayanan sirri kan motsin ’yan bindigar sun yi musu kwanton ɓauna tsakanin garuruwan Gora da Gidan Barau.
Bayan arangamar farko, wasu daga cikin ’yan bindigar sun sake dawowa wurin domin kwashe gawarwakin abokan su, amma sojojin suka sake yi musu wani kwanton ɓauna.
You must be logged in to post a comment Login