Connect with us

Labarai

DSS ta kama tarin makamai da aka yi fasa-kwaurinsu

Published

on

Hukumar Tsaro ta DSS ta yi nasarar cafke wasu tarin makamai da alburusai da ake zargin an yi safararsu ne daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya.

 

Makaman wadanda su ka hadar da bindigogi kirar AK-47 guda 21 da manyan bindigogi samfurin PKT guda huɗu an yi nasarar kama su ne a Jihar Sokoto.

 

An gudanar da samamen ne a ranar Talata, 10 ga Nuwamba, a Dawakawa, cikin Ƙaramar Hukumar Goronyo ta jihar, inda aka kai harin kan wasu hanyoyin sadarwa da ake zargin ana safarar makamai ta kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.

 

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa waɗanda ake zargin masu safarar makaman ne sun yi amfani da raƙuma wajen jigilar makaman ta wasu hanyoyi masu nisa da kuma wurare masu wahalar bi, domin kauce wa bincike daga jami’an tsaro.

 

Ana zargin cewa an shirya kai waɗannan makamai ne ga ƙungiyoyin ‘yan ta’adda da ke aiki a Arewa maso Yammacin Nijeriya, inda ayyukan ’yan bindiga, garkuwa da mutane da hare-hare kan al’umma ke ci gaba da zama babban ƙalubalen tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!