Connect with us

Labarai

Najeriya ta bukaci India ta tabbatar da walwala da kare yan kasar ta da tsare a gidajen Yari

Published

on

Gwamnatin Najeriya ta bukaci ƙasar India da ta tabbatar da walwala, mutunci da kuma kare haƙƙoƙin ‘yan Najeriya da ke tsare a gidajen yari daban-daban a ƙasar.

 

Ministar Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu, ce ta yi wannan kiran yayin ganawa da tawagar hukumomin kare haƙƙin bil’adama na Najeriya da Indiya a ma’aikatar harkokin wajen ƙasar da ke Abuja.

 

A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar, Oluwafemi Adeniyi ya fitar, ministar ta nuna damuwa kan yadda ake kula da ‘yan Najeriya da ke zaman gidan yari a Indiya, inda ta bukaci gwamnatin ƙasar ta tabbatar ana mutunta haƙƙoƙinsu tare da kula da jin daɗinsu.

 

Ta ce yarjejeniyar fahimtar juna da hukumomin kare haƙƙin bil’adama da ƙasashen biyu suka kulla, zai taimaka wajen inganta haɗin gwiwa, tabbatar da samun adalci da kuma kare mutanen da ke cikin mawuyacin hali.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!