Labarai
Sojojin Amurka 100 sun iso Najeriya don taimakawa wajen yaƙi da ƴan ta’adda

Shalkwatar tsaro ta tabbatar da isowar sojojin Amurka su 100, don taimaka mata a yaƙin da ta ke da ƴan ta’addar da ke kaiwa jama’a hare-hare.
Kakakin shalkwatar tsaron kasar nan Manjo Janar Samaila Uba ne ya bayyana hakan da ya ce Sojin na Amurka, ba za su shiga fagen daga don yin yaƙi ba, sai dai zasu gudanar da aikin horar da dakarun kasar nan na dabarun yaƙi da ƴan ta’adda.
Zuwan na sojojin Amurka ya biyo bayan tun farko Donald Trump ya zargi kasar nan da gazawa wajen baiwa Kiristoci kariya daga hare-haren da ‘ƴanta’addan da ya kira da Musulmai ke kaiwa a sassan ƙasar.
Sai dai tuni gwamnatin Najeriya ta musanta wannan zargin bayan da ta ce ƴan ta’addan na kashe dukkanin ɓangarorin Musulmai da kuma Kiristoci kuma dakarunta na aiki tuƙuru wajen yaƙi da su musamman a yankin arewa maso yammaci da kuma arewa maso gabas.
You must be logged in to post a comment Login