Labarai
Sojojin da suka yi juyin mulki a Guinea Bissau sun kullo dukkan iyakokin kasar

Sojojin da suka kifar da gwamnati a Guinea-Bissau a jiya Laraba sun tsare shugaba Omar Sussoko Embalo da wasu manyan jami’an gwamnatinsa tare da rufe kan iyakoki, kwana guda gabanin sanar da sakamakon babban zaɓen ƙasar daya janyo taƙaddama, lamarin da yanzu haka ya hana masu aikin sanya ido a zaɓen barin ƙasar, cikin su har da tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan.
Tsohon shugaban kasar nan, Goodluck Jonathan, da takwaransa na Mozambique Filipe Jacinto Nyusi na daga cikin mahimman mutanen da ke sanya ido a zaɓen da suka maƙale a ƙasar sakamakon rufe iyakoki.Tawagar da ECOWAS da Tarayyar Afirka ta kafa don aikin sanya ido a zaben Guinea Bissau ta caccaki dakatar da sanar da sakamakon babban zaɓen ƙasar da ma kifar da gwamnati da sojojin suka yi.
Wata majiyar soji ta ce tuni aka kama shugaba Omaro Sissoco Embalo, wanda ake sa ran shi zai lashe zaɓen da ya gudana don yin wani wa’adi.
Bugu da ƙari, wani babban hafsan sojin ƙasar ya ce an tsare Embalo ne tare da shugaban ma’aikatan fadarsa da kuma ministan cikin gida.
You must be logged in to post a comment Login