Ƙetare
Sojojin Kasar Niger sun tabbatar da juyin Mulki a kasar
A daren jiya laraba ne dakarun sojin Jamhuriyar Nijar suka sanar da hambarar da gwamnatin Muhammad Bazoum sa’oi bayan rade-radin yiwuwar juyin Mulki.
Rundinar sojin tabakin Kakakin ta Manjo Ahmadou Abdrahamane ne ta sanar da juyin mulkin,sakamakon abunda suka kira da halin rashin tsaro Nijar din ke ciki, da kuma halin rashin tabbas da suka ce tattalin arzikin kasar ya shiga.
Haka kuma Sun sanar da rushe kundin tsarin mulkin ƙasar, hadi da kulle dukkanin iyakokin kasar.
Kawo yanzu dai Babu labarin halin da Mohamed Bazoum ke ciki.
Yanzu haka dai sojin sun sanar da dokar Hana fita daga karfe 10 dare zuwa karfe 6 na safe.
Wannan dai shine juyin mulki na huɗu da kasar Nijar din ta fuskanta tun bayan samun ‘yancin kai daga kasar Faransa a shekarar 1960, bayan yunkurin juyin mulkin da dama da ba ayi nasara ba a kasar.
Rahoton: Yusuf Sulaiman
You must be logged in to post a comment Login