Kiwon Lafiya
Sojojin Najeriya na fafatawa da yan kungiyar boko haram a jihar Borno
Runsunar sojan kasar nan ta ce, sojojin ta na fafatawa da ‘ya’yan kungiyar Boko Haram wanda suka kai hari kan rundunar dake Baga a karamar hukumar Kukawa dake jihar Borno.
Bayanin hakan na kunshe cikin sanarwar da rundunar ta buga a shafin ta na Twitter cewa sojojin na maida martani kan harin da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai wa Bataliya ta 7 dake yankin.
Wannan nan dai shi ne karu na uku da rundunar sojan kasar nan ke maida martani ga kungiyar Boko Haram bayan da suka yi yukurin kan sojojin ta dake Baga.
Da karfe 6 na yammacin jiya Laraba ‘yan tada kayar bayan suka kai hari kan bataliya ta 6 yayin da sojojin suka sami nasarar kashe 7 daga cikin su.