Labarai
Sojojin Nijar sun ceto ƴancirani 50 da suka maƙale a hanyar Libya

Sojojin Jamhuriyar Nijar sun samu nasarar ceto ƴancirani guda 50 da suke maƙala a sahara a hanyarsu ta tafiya ƙasar Libya.
RFI ta ruwaito cewa mutanen sun maƙale ne a kusa da bakin iyakar shiga ƙasar ta Libya bayan motarsu ta lalace a ranar 10 ga watan Agusta.
“Motarsu ta lalace ne a hanyarsu ta tafiya Libya, ƙasar da ake ratsawa domin tafiya ƙasashen turai. A ciki akwai fasinjoji 44 kuma motar tana tafiya ne a hanyar Madama-Dao da ke arewacin Nijar a lokacin da ta lalace, ta tsaya cak,” in ji rahoton na RFI.
Daga baya ne aka shiga neman motar, inda sojojin suka samu nasarar ceto su, sannan aka kai su garin Madama, inda ake cigaba da kula da su.
Sai dai har yanzu ba a tabbatar da asalin ƙasashen da mutanen suka fito ba, da kuma asalin ƙasar da suke shirin zuwa.
You must be logged in to post a comment Login