Connect with us

Labarai

Sojojin sun ceto mutane 66 da aka sace

Published

on

Rundunar sojin kasar nan, ta ceto mutane sittin da shida da aka yi garkuwa da su, tare da hallaka ’yan ta’adda da dama a wasu hare-haren da ta gudanar a sassan kasar cikin mako guda.

Rundunar ta ce ayyukan sun gudana ne daga 11 zuwa 17 ga watan Satumba, a matsayin wani bangare na matakan da take dauka na yaki da ’yan ta’adda da masu aikata laifuka.

Daraktan yada labaran rundunar sojin Michael Onoja, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar kan nasarorin da sojojin suka samu.

Ya ce dakarun sun kuma kama wasu da ake zargi da aikata laifuka, tare da kwato makamai da alburusai.

Bugu da kari, rundunar ta ce ta tarwatsa hanyoyin samar da kayayyaki da bayanai ga ’yan ta’adda, tare da lalata bama-bamai 12 da aka binne a wurare daban-daban.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!