Connect with us

Labarai

’Yan ta’adda Goma Sha Bakwai sun mika wuya ga Sojoji a Jihar Borno

Published

on

Rundunar Sojin kasar nan ta ce ’yan ta’adda goma sha bakwai ne suka mika wuya ga dakarunta a jihar Borno.

Rundunar ta ce hakan na daga cikin nasarorin da dakarunta suka samu yayin ci gaba da gudanar da hare-haren da ake yi kan ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka a sassan kasar.

Daraktan yada labarai na ayyukan tsaro na rundunar, Manjo Janar Michael Onoja, ne ya bayyana hakan a cikin bayanin mako-mako kan ayyukan sojoji.

Ya ce tsakanin ranar 4 zuwa 10 ga watan satumba, sojojin sun kuma tarwatsa hanyoyin samar da kayayyaki ga ’yan ta’adda, tare da cafke harsasai 300.

Haka kuma, rundunar ta ce dakarunta sun samu nasarar kubutar da wasu mutane da aka yi garkuwa da su a wasu sassan ƙasar.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da kai hare-hare domin dakile ayyukan ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun laifuka.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!