Labaran Wasanni
Spain ta kawo karshen wasanni 37 da kasar Italiya ta yi ba a doke taba
Kasar Sifaniya karkashin jagorancin Luis Enrique ta kawo karshen wasanni 37 da Kasar Italiya ta yi ba’a doke ta ba.
Kasashen biyu dai sun fafata a ranar Laraba 06 ga Oktoban 2021 a gasar kasashen turai mai taken Nations League a wasan kusa da karshe da Sifaniya ta yi nasara da ci 2-1.
Mikel Arteta ka iya rasa aikin sa idan Arsenal ta yi rashin nasara a wasanni uku masu zuwa
Tin da fari dan wasan Manchester City Ferran Torres ne ya fara zura kwallon farko tun kafin zuwa hutun rabin lokaci a mintuna na 17.
Kana dan wasa Torres din ya sake zura kwallo ta biyu a minti na 45.
Sai dai dab da kammala wasan dan wasan kasar Italiya Pellegrini ya zura kwallo guda a minti na 83.
Rashin nasarar da kasar ta Italiya ta yi ya kawo karshen wasanni 37 ba tare da anyi nasara akan taba karkashin jagorancin Roberto Mancini.
Haka kuma karo na farko da aka zurawa mai tsaran gidan kasar Gianluigi Donnarumma kwallo biyu a wasa guda guda tun san da ya fara bugawa kasar wasa shekaru biyar da suka gabata.
Kawo yanzu dai kasar Sifaniya zata buga wasan karshe na gasar ta Nation League tsakanin Belgium ko Faransa a wasan karshe a ranar Lahadi 10 ga Oktoban da muke ciki.
You must be logged in to post a comment Login