ilimi
SSANU da NASU sun shirya tsunduma yajin aiki
Ƙungiyar manyan ma’aikatan Jami’oi SSANU da takwararata ta ma’aikatan jami’a da waɗanda ba malamai ba watau NASU, sun bayyana cewa sun shirya tsunduma yajin aiki a Litinin ɗin makon gobe.
Rahotonni sun tabbatar da cewa ƙungiyoyin sun cimma matsayar ne a ƙarshen wani taron da suka yi ranar Lahadi a birnin Akure na jihar Ondo.
Sun ce za su shiga yajin aikin ne a matsayin na gargaɗi har na tsawon mako guda domin neman gwamnati ta biya wasu haƙƙoƙinsu.
BBC ta ruwaito cewa, cikin buƙatun ƙungiyoyin har da batun rashin biyan albashinsu na wata 4 da gwamnatin ba ta yi ba lokacin da suka shiga yajin aiki a shekarar 2022.
Haka kuma Ƙungiyoyin sun nuna rashin jin daɗinsu kan rashin biyan mambobinsu albashin duk kuwa da cewa gwamnatin tarayya ta biya takwarorinsu na malaman jami’oi nasu kuɗaɗen.
You must be logged in to post a comment Login