Labarai
SUBEB za ta shigar da Almajirai tsarin ilimi na BESDA – Danlami Hayyoo
Hukumar kula da ilimin bai-daya ta Jihar Kano SUBEB ta ce za ta shigar da almajiran tsangaya cikin tsarin nan na Better Education Service Delivery for all BESDA, da ke layi daya da ilimi kyauta Kuma wajibi.
Shugaban hukumar Dr Danlami Hayyo ne ya bayyana hakan a yau lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan fitowa daga tattaunawa da gwamnan Kano a fadarsa.
Dr Hayyo ya kara da cewa yayin zantawar, gwamnan ya amince da kafa kwamiti wanda mataimakinsa Nasiru Yusuf Gawuna zai jagoranta da sauran mambobin da suka hada da kwamishinan ilimi.
Danlami Hayyo ya kuma ce kwamitin zai tattauna tare da duba yiwuwar yi wa almajirai ‘yan asalin Jihar Kano rajistar tsarin.
Wakiliyarmu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa kafin tattaunawar ta su sai da gwamnan ya kara jaddada cewa ilimi kyauta ne a Kano kuma wajibi, sannan za a gyara tsarin karatun almajirai.
You must be logged in to post a comment Login