Labarai
SWAN ta karrama ɗan wasa Kamalu Sani

Kungiyar Marubuta labaran wasanni ta Najeriya SWAN reshen jihar Kano, ta karrama dan wasan motsa jiki na Gymnastics Kamalu Sani da ya wakilci jihar Kano tare da lashe mata lambobin Zinare biyu a gasar wasannin matasa ta kasa National Youth Games, da aka kammala a birnin Asaba na jihar Delta.
Haka zalika kungiyar ta bawa matashin dan wasan kyautar Kudi Naira Dubu Ashirin,don karfafa masa Gwiwa.
Taron karramawar da karawa juna sa ni ya gudana ne a harabar ofishin ‘yan jaridu na jiha NUJ, a wani bangaren na bikin murnar cikar kungiyar ta SWAN shekaru 60 da kafuwa.
You must be logged in to post a comment Login