Labarai
Ta’addanci : An yiwa wasu manoma yankan Rago a jihar Katsina
Rahotanni daga jihar Katsina na cewa ‘yan fashi sun yiwa manoma bakwai yankan rago tare da yin gaba da wasu mutum 30 a karamar Hukumar Sabuwar jihar Katsina.
Dan Majalissar dokokin jihar Katsina mai wakiltar mazabar Sabuwa Hon Ibrahim Kaka Machika shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a jiya Litinin.
A cewarsa wannan ibtila’I ya faru ne a kauyukan Tashar Bama, Dogon Mu’azu da kuma Unguwar Maigayya.
Za mu cigaba da bibiyar wannan labarin a cikin shirye-shiryenmu na gaba.
You must be logged in to post a comment Login