Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Ba a zabe ni don in rika biyan albashi ba – El-Rufai

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya ce, al’ummar jihar Kaduna sun zabe shi ne don ya rika gudanar musu da ayyukan raya kasa da za su ciyar da jihar gaba, ba wai don ya rika biyan albashi ba.

 

Wannan na zuwa ne a lokaci guda da gwamnatin jihar ta sallami wasu ma’aikatan kananan hukumomi 4000 daga kananan hukumomi 23 da ke jihar

 

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan Muyiwa Adekeye, ta ce, an zabi gwamnan ne domin ya daidaita tsakanin marasa galihu da masu hannu da shuni da ke jihar, da kuma gina sabbi tare da gyaran makarantu da suka lalace, gyara asibitoci, kwaskware abubuwan more rayuwa.

 

Nasir El-Rufai a cewar sanarwar, burin sa shine mai da jihar ta zama abin sha’awa ga masu son zuba jari na ketare da na cikin gida.

 

Sanarwar ta kuma ce kudade da gwamnati ke kashewa wajen biyan albashi yana kara yawa, ya yin da a bangare guda, kudaden da gwamnatin jihar ke karba daga asusun tarayya raguwa ya ke.

 

Gwamna El-Rufai ta cikin sanarwar dai ya kuma ce a watan Nuwamban shekarar 2020, gwamnatin jihar Kaduna ta karbi jimillar naira biliyan 4.83 daga asusun tarayya, ya yin da ta biya albashin naira biliyan 4.66 wanda, abin da ya rage a hannunta da za ta yi ayyukan raya kasa shine naira miliyan 162.9.

 

Haka zalika ya ce, a shekara da ta gabata 2020 duk kudade da gwamnatin jihar ta karba daga asusun tarayya albashi ta rika biya da su, da dan wasu bukatu na kunji-kunji, wanda wasu lokutan ma kudaden ba sa iya biyan bukatun albashin gaba daya.

 

‘‘A watan Maris bayan da muka biya albashi abin da ya rage mana shine naira miliyan 321 kacal’’ a cewar El-Rufai.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!