Labarai
Tabarbarewar tsaro : Mun bukaci a sanya dokar tabaci a jihohin Arewa
Gamayyar kungiyoyin kishin alummar Arewacin Najeriya CNG, ta gabatarwa rundunar ‘yan sandan Kano takardar bukatar samar da ingantaccen tsaro.
Ta cikin takardar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar ta CNG, sun bukaci gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki akan harkokin tsaro da su sanya dokar ta baci kan halin tabarbarewar tsaro a jihohin Arewacin Najeriya.
Kungiyar ta CNG ta bukaci hakan ne a yau Asabar yayin da mambobinta suka yi tattaki zuwa shalkwatar yan sandan jihar Kano domin gabatar mata da bukatunta a rubuce.
Da yake jawabi a madadin hadakar kungiyoyin, Kwamared Nastura Ashir Shariff, ya ce, sun ziyarci shalkwatar yan sandan ne domin shaida wa rundunar yan sandan yadda ya kamata a kyautata rayuwar jamian tsaron kasar nan domin karfafa musu gwiwa wajen gydanar da aikinsu.
Haka kuma ya kara da cewa ya kamata a yiwa dakarun tsaro na SWAT da aka maye gurbin jamian tsaro na SARS kasancewar an fara samun aikata taaddanci a wasu sassan NaJeriya, dom haka akwai bukayar yin duba na tsanaki kan harkar tsaro.
A nasa jawabin, kwamishinan yan sandan jihar Kano Habu Ahmad Sani wanda shi ne ya tarbi yan kungiyoyin ya ce, ya karbi takardar tasu kuma zai mika ta wajen da ya dace.
Kwamishinan yan sandan na Kano ya kuma bayyana wa yan kungiyar wasu daga cikin irin nasarorin da rundunar yan sandan ta samu na dakile ayyukan ta’addanci.
You must be logged in to post a comment Login