Connect with us

Labarai

Tajudeen Abbas ya rushe dukkan kwamitocin wucin-gadi na Majalisar Wakilai

Published

on

Shugaban majalisar wakilai Tajudeen Abbas, ya bayar da umarnin rushe dukkan kwamitocin wucin-gadi na Majalisar.

 

Matakin ya fara aiki daga ranar 28 ga Agusta, 2026, bayan wa’adin da aka bai wa kwamitocin ya kare.

 

Majalisar ta ce an bai wa kwamitocin wa’adin kammala ayyukansu da gabatar da rahotanni, amma lokacin ya wuce.

 

An kuma umarci shugabannin kwamitocin da su mika duk wasu rahotanni da takardun da suka rage ga ofishin magatakardar Majalisar.

 

Daga yanzu, duk wani aiki da ake yi da sunan kwamitocin da aka rushe ya kamata ya tsaya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!