Labarai
Shugaba Tinubu ya bukaci shugabanni su fifita bukatun al’umma kan bukatun kansu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci shugabanni a matakai daban-daban da rika fifita bukatun al’umma kan bukatun kansu.
Tinubu ya ce Najeriya na bukatar shugabanni masu kishin kasa, wadanda za su sadaukar da kansu wajen yi wa al’umma hidima da kuma kawo ci gaba.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen bikin cika shekaru 70 da haihuwa na tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, da aka gudanar a Yola, Jihar Adamawa.
Tinubu, wanda sakataren gwamnatin tarayya George Akume, ya wakilta, ya ce ya kamata shugabanni su dauki matakin hidimtawa al’umma da ci gaban kasa a matsayin babban abin da ya fi muhimmanci.
You must be logged in to post a comment Login