Labarai
Jam’iyyar APM ta zargi Tinubu da rashin kwarewa kan matsalar tsaro

Jam’iyyar APM ta zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin kwarewa wajen magance matsalar tsaro a kasar nan.
Jam’iyyar ta ce gwamnatin na kokarin nuna cewa tsaro ya inganta, alhali kuwa har yanzu ana fama da kashe-kashe, garkuwa da mutane da hare-haren ’yan bindiga a sassan kasar.
APM ta kuma yi ikirarin cewa rahoton Global Terrorism Index na 2026 ya sanya Najeriya a matsayi na hudu cikin kasashen da matsalar ta’addanci ta fi tsanani a duniya.
Jam’iyyar ta ce gwamnatin Tinubu ba ta da cikakken tsari da za ta bi wajen kawo karshen matsalar rashin tsaron.
You must be logged in to post a comment Login