Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

 Talauci da annobar corona sun ƙara ta’azzara take haƙƙin ɗan adam – Shehu Abdullahi

Published

on

Hukumar kare haƙƙin ɗan adam ta ƙasa ta alaƙanta talauci da annobar corona a matsayin abinda ya ta’azzara cin zarafin ɗan adam.

Shugaban hukumar shiyyar Kano Malam Abdullahi Shehu ne ya bayyana hakan ta cikin Labaran Mu leƙa mu gano na Freedom Radio a ranar Alhamis.

Tattaunawar ta mayar da hankali kan bikin ranar yaƙi da cin zarafin ɗan adam da majalisar ɗinkin duniya ta ware duk ranar 10 Nuwamba.

Malam Abdullahi Shehu ya “A shekarar 2021 daga watan Janairu zuwa kwanaki 18 ga watan Nuwamba rahotanni sun nuna yadda ake samun karuwar cin zarafin ɗan adam da yawan su ya kai 835″.

“Mafi yawan ƙorafin da muke samu na ma’aurata ne, sakamakon halin da aka tsinci kai na matsin tattalin arziƙi dalilin annobar corona wanda hakan ke haifar da rikici a tsakanin su” a cewar shugaban.

Ya ci gaba da cewa “daga shekarar 2017 an samu hawa da saukar rahotannin ta ke haƙƙin ɗan adam da cin zarafin sa, sai dai rahotannin fyaɗe shi ne babban ƙalubale mafi muni da muke samu, musamman yadda ake tsangwamar waɗanda suka riski kan su a ciki sakamakon tasirin al’adun da al’umma ke gudanarwa”.

“Yadda Mata da ƙananan yara ke fuskantar cin zarafi, abu ne da bai da ce ba, sai dai muna ƙoƙari da zarar mun samu rahoto irin wannan mu miƙa shi ga jami’an lafiya don gudanar da bincike” a cewar Shehu Abdullahi.

Wannan dai na zuwa ne a wani ɓangare na gudanar da ayyuka na kwanaki 16 gabanin bikin ranar kare hiƙƙin ɗan adam ta duniya, da kan mayar da hankali wajen wayarwa da jama’a kai dongane da ƙalubale da cin zarafi da ƴaƴa mata da ƙananan yara suka fi fuskanta.

Bikin na bana za a fara daga ranar 25 ga Nuwamba zuwa 10 ga Disambar 2021 don gudanar da bukukuwa tattaki da sauran shirye-shirye don kawo ƙarshen matsalar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!