Labarai
Talauci ne ya jefa matasan Najeriya cikin harkar shaye-shaye – SEDSAC
Daga Hafsat Abdullahi Danladi
Kungiyar da ke rajin kare samar da shugabanci na gari da bunkasa harkokin dimukradiyya da ci gaban matasa SEDSAC ta bayyana damuwarta kan yadda talauci ya zamo silar tabarbarewar tarbiyyar matsana wannan lokaci.
Shugaban kungiyar kwamared Umar Hamisu Kofar Naisa ne ya bayyana hakan yayin taron da kungiyar ta shiryawa matsa na tunatar da su irin rawar da za su taka don ciyar da kasar nan gaba a ani bangare na bikin cika shekara 60 da kasar nan ta yi a yau.
Ya ce, lokaci yayi da matasan kasar nan za su tsame kan su daga shiga harkokin shaye shaye tare da mayar da ahankali wajen samun ingantaccen ilimin da zai zamo tsani na canja yanayin shugabancin kasar nan.
Wasu matasa da suka halarci taron sun bayyana irin abubuwan da suka amfana da shi a yayin taron musamman yadda za su tsaya da kafafun su na ganin saun kawar da kai daga miyagun dabi’u da kuma yadda za su inganta rayuwarsu..
Wakiliyarmu Hafsat Abdullahi Danladi da ta halarci taron ta ruwaito cewa, taron ya samu halarta matasa daga sassa daban daban na jihar kano inda aka tattauna muhimman batutuwan da za su inganta rayuwar su.
Taron wanda aka yiwa take da : fito da hanyoyin da za a yaki talauci da kuma kuncin rayuwa.
You must be logged in to post a comment Login