Labarai
Tanzania: Masu zanga-zanga sun sake mamaye kan tituna

Masu zanga-zanga sun sake fitowa kan tituna a Tanzaniya karo na uku, duk da gargadin da hafsan sojin kasar ya yi musu na su dakatar da tarzomar da rikici.
Zanga-zangar ta barke a manyan birane inda matasa ke nuna adawa da sakamakon zaben da aka gudanar ranar Laraba, suna cewa ba a yi adalci ba domin an hana manyan ‘yan adawa yin takara da shugabar kasa Samia Suluhu Hassan.
Har yanzu intanet ɗin kasar a katse yake, abin da ke hana samun sahihan bayanai kan mutuwar mutane, yayin da hukumomi suka tsawaita dokar hana fita domin rage tarzomar.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga jami’an tsaro na kasar da su guji amfani da karfi fiye da kima.
You must be logged in to post a comment Login