Labarai
Taron AU: Buhari zai tafi Ethiopia
A gobe Alhamis ne shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai bar Najeriya zuwa ƙasar Ethiopia wato (Habasha) domin yin wata ziyarar kwanaki huɗu a birnin Addis Ababa na ƙasar.
Shugaban zai halarci taron shugabannin ƙasashen Afirka karo na 35.
Mai magana da yawun shugaban Buhari Femi Adesina ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abuja.
Adesina ya ce, yayin taron Buhari zai bi sahun sauran shugabannin Afirka wajen lalubo hanyoyin magance ƙalubalen siyasa da matsalolin tattalin arziƙi da zamantakewar nahiyar Afrika.
Ana sa ran shugaba Buhari zai gana da wasu shugabannin ƙasashe biyu tare don yin haɗin gwiwa wajen inganta huldar kasuwanci, da haɗa kai don tinkarar ƙalubalen tsaro da kuma ƙulla alaƙar kasuwanci domin samun ci gaba mai ɗorewa.
Adesina ya ce shugaban zai samu rakiyar Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama da ministan Lafiya Dakta Osagie Ehanire da ministan Noma Mohammed Abubakar sai ministan harkokin Agaji da ci gaban Jama’a, Sadiya Umar Farouk.
Sauran su ne mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da darakta janar na hukumar leken Asiri ta ƙasa Ahmed Rufa’i.
You must be logged in to post a comment Login