Kiwon Lafiya
Taron majalisar zartawa ta kasa ta amince da fitar da fiye da naira biliyan 61 gon gyara hanyoyi
Taron majalisar zartarwa ta kasa a jiya ya amince da fitar da naira biliyan 61 da miliyan 464 domin gyaran hanyoyi, da kuma yasar bakin teku da gina gidaje mallakar gwamnatin tarayya.
Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola da kuma ministan sufuri Rotimi Amaechi da kuma ministan cikin gida Abdurrahman Dambazau da kuma na Albarkatun ruwa Silaiman Adamu ne suka sanar da hakan ga manema Labarai jim kadan bayan kammala zaman majalisar na jiya.
Amaechi ya ce majalisar ta kuma amince da fitar da biliyan 13 domin aikin yin yasa a bakin teku da ke warri.
A cewar Fashola ma’aikatar sa ta samu amincewar ba da kwantiragin har guda hudu da suka hadar da gina hanyar Babalapa zuwa Sharam da ke jihar Plateau da zata lakume naira biliyan 19 da miliyan 92 sai kuma hayar da ta tashi daga Lagos zuwa Otta da zata lakume biliyan 22.
Haka kuma ma’aikatar zatayi aikin ginin hanyar da ta tashi daga Fatakwal zuwa Enugu da zata lakume naira biliyan 56 da