Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tasirin Kwankwaso a Kano kaɗai ya ishe mu – Saƙon Doguwa ga Ganduje

Published

on

Shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya Alhasan Ado Doguwa ya ce rigimar tasirin Kwankwaso a siyasar Kano kaɗai ta ishi jam’iyyar APC idan ba a samu ɗinke ɓarakarta ba.

Doguwa na martani ne kan zargin da ake masa na yiwa Mataimakin ɗan takarar Gwamnan APC a Kano Murtala Sule Garo rauni.

Ya ce “Ba za a ɗinke ɓaraka ba sai Gwamnan Kano ya yarda kowa ɗansa ne, sai Ganduje ya yarda Murtala ɗa ne, muma ƴaƴa ne, domin muna fuskantar muguwar barazana daga abokan hamayya”.

“Kowa ya san tasirin da tsohon Gwamna Kwankwaso ya ke da shi a jihar Kano, wannan rigimar kaɗai ta ishe mu”.

Alhassan Ado dai ya musanta cewa shi ne ya yiwa Murtala Garo rauni, inda ya ce sun dai yi cacar baki, amma zamewa Murtalan ya yi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!