Labarai
Tasirin talla ga ‘ya’ya Mata
An fi lura da cewa, iyaye mata ke dorawa ‘yara talla musammama ‘yan-mata, ba tare yin la’akari da lokutan zuwa makaranta ba, wanda hakan ke baiwa yaran kwarin gwiwar kin zuwa makaranta, sakamakon riban da suke samu.
Haka zalika, wasu iyayen kan nuna cewa da talla yarinya za ta tara abun da za a kai ta daki da shi, wanda da dama ke ganin babban aban abun takaici ma,
Bincike da Freedom Rediyo ta yi, ya nuna cewa, talla na daga cikin abubuwan da ke janyowa ‘yara mata matsala, wanda har ta kai ga an lalata musu rayuwa.
Haka kuma tashar Freedom radiyo ta ji ta bakin wasu ‘yan-mata da ke a kwayar birin Kano, kan dalilin da yasa suke talla, suna mai cewar dole ce ta sanya su daukar tallan ba dare ba rana
Jima’i da mata akai- akai na maganin bugun zuciya.
Kungiyar iyayen yara: ‘ya’ya 47 aka sace mana
Zaurawa sun yi bore kan hana zancen dare a Kano
Mun ji ta bakin daraktar al’amuran yara ta ma’aikatar kula da harkokin mata da ke nan Jihar Kano, Hajiya Binta Nuraini, inda ta ce, akwai dokar da ta basu damar kama duk iyaye da suka bar yaran su suna talla, sannan su gurfanar da su.
Shugaban wata kungiya mai zaman kanta Mafita dake rajin dakile talla tsakanin yara, Mukthar Baba ya bayyana yadda suke bi wajen taimakawa yara baya ga hana su yin talla, ta yadda suke basu jari da zai taimaka musu.
Binciken da masana suka gudanar ya nuna cewa, Talla a wajen ‘yan-mata a kwaryar birnin da karkara a nan Jihar Kano ya zama ruwan dare, sakamakon fatara da san rufawa kai asiri.
An kuma lura cewa, jihohin Arewacin kasar nan, sun fi kowanne samun ‘yan-talla musammama ‘yan-mata, wandanda ke fuskantar kalubalen daban-daban daga masu sayen kayayyakin na su.