Manyan Labarai
Maganin bugun zuciya.
Bayan nishadi da jin dadi bincike ya nuna cewa yawan yin jima’i yana kara lafiya da kare garkuwar jiki.
Ba wannan kadai ba , hatta cutar daji da tayi katutu tsakanin al’umma saduwa da mata na maganin cutar ta daji.
A lokacin da muke ciki a yanzu zaka samu cewa wasu mutanen suna fama da cutar rashin isasshen bacci, wanda rashin isasshen baccin, na sanadin kawo damuwa tsakanin mutane da hawan jini ,ka san cewa jima’i na maganin rashin bacci.
Ba anan alfanun na jima’i ya tsaya kadai ba, hatta gajjiya da yawan kasala ,jima’in yana maganin sa da kuma karawa mutum farin ciki da walwala tsakanin al’umma da yake mua’amla da su yau da gobe.
A wani sabon bincike da ya bayyana kwanannan. Jima’i na maganin bugun zuciya da kan samu al’umma ,sannan yana tabbatar da mutum a matsayin sa yadda yake so da kuma halittar tsarin jikin sa ba tare da wasu matsaloli ba.
Saboda haka shi jimai wata hanya ce da jinsin na mace da namiji zasu amfana gaba daya , kuma yana daga cikin magani mafi kyau da Allah madaukakin sarki ya halittarwa halittun sa..
Sabon binciken ya nuna cewa tsakanin mutane 1,165 ‘’yan shekaru 40 da 70 binciken ya bibiyi tarihin lafiyar wadannan mutane masu wadannan shekaru domin gano dangataka tsakanin jima’i da ciwon zuciya.
Binciken ya gano cewa mutanan da suka fi yawan aikata jima’i sune mafi kasa da kamuwa da cutar ciwon zuciya .
Binciken na da matukar muhimmanci saboda wadanda suka yi binciken sun kula da wasu abubuwa masu muhimmanci kamar lafiyar dan Adam, daidaituwar jini, dabi’ar shan taba ko akasin haka , ko mazan na shan taba ko akasin haka, sannan bincike ya tabbatar da cewa Jima’i shi kadai na dakile hadarin kamuwa da bugun zuciya.
Wani mai bincike a harkokin Jima’i da Dr Justin Lehmiller ya gabatar yace akwai wani abu na musamman game da aikata jima’i musamman ma idan hakan ta shafi lafiyar zuciya.
Dr Lehmiller ya kara da cewa dalilin da yasa jima’i yake kawo lafiyar zuciya saboda wani bangare ne na motsa jiki kuma yana da karfi wajen magance gajiyya wanda abu ne mai kyau.
A wani bincike da jamiar Princeton ta gudanar tace yin jima’i a kullum yana girmar da halitittun kwakwalwa wanda suke da alhakin bincikar gajiya na jikin dan Adam.
Haka kuma wani binciken ya gano cewa mazan da suke yin jimai a kullum na tsawon sati biyu na da karancin hawan jinni idan aka kwatanta da wadanda basa yi.
Sannan karancin hawan jini na nufin karancin cutar zuciya,Saboda haka ya kamata maza su kara kwazo wajen samun jima’i akai akai saboda dalilan lafiya.