Labaran Wasanni
Tennis: Ashleigh Barty ba za ta buga wasan karshe a gasar WTA ba
Lamba daya ‘yar kasar Birtaniya Ashleigh Barty, ba za ta samu damar kare kambun gasar WTA da ta lase a shekarar 2019 ba, sakamon killace kanta da za ta yi da ga kamuwa da cutar Covid-19.
Wasan karshen dai za a gudanar da shi a watan Nuwambar shekarar da muke ciki ta 2021.
Dan wasan Nigeria Victor Osimhen zai iya zama dan wasan Duniya-Luciano Spalletti
Hakan ya sa ‘yar wasan za ta koma kasar Australia domin tin karar gasar Australian Open.
‘Yar wasa Ashleigh Barty dai itace ta lashe gasar WTA a shekarar 2019 bayan bullar cutar coronavirus.
Barty dai a shekarar 2021 da muke ciki ta lashe gasanni biyar ciki har da ta Wimbledon.
Yanzu dai za ta mai da hankali domin buga gasar Australian Open a yankin Melbourne Park, wanda ake saran farawa daga Watan Janairun shekarar 2022.
You must be logged in to post a comment Login