Connect with us

Labarai

Tinubu: Sauye-sauyen gwamnati sun farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya

Published

on

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce a lokacin da ya hau karagar mulkin ƙasar, tattalin arzikinta na dab ta durƙushewa saboda abin da ya kira tsare-tsare tattalin arziki marasa ɗorewa.

Cikin jawabin da ya yi wa ƙasar albaracin cikarta shekara 65 da smaun ƴancin kai, Shugaba Tinubu ya ce matakan da gwamnatinsa ta ɗauka ne suka taimaka wajen ceto ƙasar daga durƙushewar;

”A ƙarƙashin gwamnatinmu tattalin arzikin ya fara farfaɗowa sakamakon sauye-sauyen da muka ɓullo da su shekaru biyu da suka gabata”, in ji shi.

Shugaban na Najeriya ya ce a rubu’i na biyu na shekarar 2025 arzikin da ƙasar ke samu a cikin gida ya haɓaka da kashi 4.23, mafi yawa cikin shekara huɗu, inda ma ya zarta hasashen da IMF ta yi.

”Hauhawar farashin kayayyaki ta ragu zuwa kashi 20.12 cikin 100 a watan Agustan da ya gabata, raguwa mafi yawa cikin shekara uku”, kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa na aiki tuƙuru domin bunƙasa fannin noma don wadata Najeriya da abinci da kuma sauko da farashin kayan abinci a faɗin ƙasar.

Haka ma shugaban na Najeriya ya ce ƙasar ta samu bunƙasar da ba a taɓa gani ba wajen tara kuɗin shiga a fannin da na mai ba.

”Zuwa watan Agustan 2025 mun samu kuɗin shiga a fannin da ba na mai ba, da ya kai naira tiriliyan 20. A watan Satumba kaɗai mun samu naira tiriliyan 3.65, ƙarin kashi 411 kan abin da aka samu a watan Mayun 2023”, in ji

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!