Labarai
Tinubu ya kafa kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC

Shugaban kasa Bola Tinubu ya kafa kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC domin tunkarar babban zaben shekarar 2027, inda ya nada tsohon Gwamnan jihar Zamfara Sanata Abdulaziz Yari a matsayin daraktan kwamitin.
Gwamnan Jihar Imo Hope Uzodimma, zai kasance Sakatare, yayin da shugaba Tinubu da mataimakin sa, Kashim Shettima za su jagoranci kwamitin a matsayin shugaba da mataimakin shugaba na farko.
Shugaban APC na kasa Farfesa Nentawe Yilwatda, zai kasance mataimakin Shugaba na biyu.
Sanata Ajibola Basiru da Hadiza Bala Usman kuma za su kasance Mataimakin sakatare da Mataimakiyar Sakatare.
You must be logged in to post a comment Login