Labarai
Yan sanda sun ceto mutane 75 da yan bindiga suka yi garkuwa da su a Kaduna

Rundunar ’Kaduna ta ce ta ceto mutane 75, ciki har da mata da kananan yara, wadanda wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a kusa da kauyen Falwaya dake karamar hukumar Birnin Gwari.
Kakakin rundunar, DSP Mansir Hassan, ya ce an sace mutanen ne a ranar 19 ga Agusta yayin da suke cikin motocin haya.
Ya ce bayan samun bayanan sirri daga kungiyar NURTW, jami’an ’yan sanda suka kai samame inda masu garkuwar suka tsere, tare da barin wadanda suka sace.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Rabiu Muhammad, ya yabawa jami’an tsaro da kungiyar Direbobi kan taimakawa wajen ceto mutanen.
Ya kuma bukaci jama’a su rika kai rahoton duk wani motsi na shakku ga jami’an tsaro.
You must be logged in to post a comment Login