Connect with us

Labarai

REMASAB ta bukaci hadin kan al’umma wajen tabbatar da tsaftar muhalli a Kano

Published

on

Hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano REMASAB ta bukaci hadin kan al’ummar jihar wajen tabbatar da tsaftar muhalli da kuma zubar da shara a wuraren da aka tanada.

 

Mai magana da yawun hukumar Malam Abubakar Ahmad ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a aka kuma rabawa manema labarai.

 

Sanarwar ta ce shugaban hukumar Dakta Muhammad S Khalil ya buƙaci al’umma, musamman masu kasuwanci da shugabannin al’umma, da su rika bin ka’idojin tsaftar muhalli tare da bai wa REMASAB cikakken hadin kai.

 

Hukumar ta ce tana ci gaba da aikin kwashe shara da tsaftace muhalli a sassa daban-daban na jihar Kano.

 

Daga cikin wuraren da aka gudanar da aikin tsaftacewar akwai magudanar ruwa ta Kasuwar Tarauni, Sabon Titin Dandago, magudanar Titin Gwarzo da dai sauran su.

 

Sanarwar ta kara da cewa Daraktan ayyuka na hukumar Alhaji Usman Shehu Kabir ne ya jagoranci aikin tsaftace wuraren.

 

Hukumar ta kuma bukaci al’ummar jihar da su guji zubar da shara a magudanan ruwa da sauran wuraren da ba su dace ba, domin taimakawa wajen kare muhalli da rage matsalar ambaliya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!