Labaran Wasanni
Tokyo 2020: AFN ta bude sansanin daukar horo a Abuja
Hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta Najeriya, AFN, ta bude sansanin horas da ‘yan wasan da za su wakilci kasar nan a gasar Olympics ta 2020.
An dai bude sansanin daukar horon ne a ranar Lahadi 4 ga watan Yuli a Abuja.
Babban Sakataren hukumar ta AFN, Adisa Beyioku, a cikin wata takarda da ya aikewa Daraktan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na ma’aikatar wasanni, ya gayyaci ‘yan wasa da masu horaswa zuwa sansanin.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, an gayyaci ‘yan wasa 25 da masu horaswa 10 don yin zango yayin da ake tunkarar wasannin Tokyo.
You must be logged in to post a comment Login