Labarai
Trump ya musanta zargin hada baki da shugaba Volodymyr Zelensky
A wani lamari da ake gani kamar fito-na-fito ne da ‘yan majalisun dokokin Amurka daga jam’iyyar Democrat, shugaba Trump kan bayyana batun tsige shi sakamakon rokon da ya yi ga takwaransa na kasar Ukraine da cewa ya binciki tsohon mataimakin shugaban kasar ta Amurka Joe Biden, da cewa abin dariya ne.
Shugaban Trump dai ya musanta zargin da ake yi masa na cewa ya hada baki da Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky da ya binciki abokin adawar sa kuma tsohon mataimakin Shugaban kasar ta Amurka, Mr. Joe Biden.
Rahotanni na nuni da cewa, ana ci gaba da samun tsamin dangantaka tsakanin Shugaba Trump da ‘yan majalisun kan batutuwa da dama.
Mista Trump yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a daren jiya Laraba a ofishin jakadancin Amurka na majalisar dinkin duniya da ke birnin New York, ya ce shi bai ga laifin komai ba kawai don ya gana da da shugaban kasar Ukraine ta wayar tarho.
Shi dai Donald Trump ya bayyana cewa bita da kullin da suke masa ba zai taba samun nasara ba.