Kiwon Lafiya
tsadar allurar rigakafin sankarau ce ta sanya ba’a ajiye ta
Wani kwararren likita a nan Kano Farfesa Auwalu Umar Gajida ya bukaci mutane da su rika yin hanzarin zuwa Asibiti da zarar sun ji wani sauyi a jikinsu, don kaucewa kamuwa da cutar Sankarau.
Farfesa Auwalu Umar Gajida wanda shi ne mataimakin shugaban kwamitin shawarwari da tuntuba kan harkar lafiya na Asibitin koyarwa na Aminu Kano da ke nan Kano, ya bayyana hakan ne a jiya ta cikin shirin Mu Leka Mu Gano na musamman na nan Freedom Rediyo.
Ya ce cutar tana yaduwa ne a tsakanin wasu daga cikin kasashen Africa, a lokutan zafi da na hunturu gabanin faduwar damuna.
Haka zalika ya kuma ce, ana rigakafin cutar amma har sai an yi gwaji kan wasu da suka kamu da ita sannan ne za’a iya gano nau’in cutar da ta kama mutanen tare da nemo rigakafin.
Farfesa Auwalu Umar Gajida, ya kuma ce cutar tana farawa ne da zazzabi da ciwon kai da sauran wasu cutuka da mutane ke daukarsu, a matsayin kananan cutuka.
Haka zalika ya kara da cewa kasancewar allurar rigakafin cutar na da matukar tsada, shi ya sanya gwamnati ba ta saya ta ajiye, har sai an yi gwaji an tabbatar da nau’inta gabanin sayo ta.