Labarai
Tsafta muka fi baiwa fifiko a sana’ar mu –Masu lemo da Mangwaro
Kungiyar masu sayar da Lemo da Mangwaro ta Kasuwar ‘Yanlemo a Kano tace suna tsaftace kayan marmarin da ake siyarwa ga mutane da kuma tsaftar kasuwar domin kare lafiyar al’umma daga kamuwa da cututtukan zamani.
Shugaban kungiyar kasuwar masu sayarda Lemo da Mangwaro Alhaji Mustafa Idi ne ya bayyana haka a yayin zantawarsa da wakilin Freedom Radio Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa.
Karin labarai:
‘Yan kasuwa su kula da tsaftace wuraren sana’ar ku-Hussam Musa Kyari
Tabbas Afakallahu na kokari wajen tsaftace Kannywood –Kamaye
Alhaji Mustafa Idi ya kara da cewa sun dauki matakin tsaftace ciki da wajen kasuwar domin ganin basu baiwa kwayoyin cuta gurin zama ba musamman yadda hukumar kwashe shara ta jihar kano ke basu goyan baya don kwashe sharar kasuwar.
Shugaban kungiyar Alhaji Mustafa Idi ya kuma nanata cewa babu wani mutum guda da kungiya zata bari ya shigo da kaya mara kyau domin a sayarwa da mutane wanda a karshe zai iya cutar da lafiyar dubban jama’a.
You must be logged in to post a comment Login